– Kungiyar ASUP tace babu wani ja da baya a
kokarin ta na shiga yajin aiki
–
Gwamnatin tarayya dai tayi kokarin a sasanta amma abin ya
ci tura
–
Sai dai wasu Makarantun sun ki shiga yajin aikin
Mr. Anderson Ezeibe, wanda shine Sakataren Kungiyar ASUP ta Malaman
Makarantun Polythechnic yace sun tafi yajin aiki na mako daya
kuma babu maganar ja da baya a kan batun na su.
Malaman Makarantun na gaba da Sakandare sun tafi yajin aikin ne a tsakar
daren jiya bayan duk wani yunkuri sasanci da Gwamnati ya ci tura. Kungiyar tace
kaf ma’aikatan na ta za su janye aiki har sai wa’adin ya kare.
Kungiyar za ta tafi yajin aikin mako guda ne a matsayin gargadi kafin idan
abubuwa sun dace su dawo, idan kuma ba haka ba to sai baba ta gani. Tun bara
dai Kungiyar ta ke kukan za ta tafi yajin aiki, sai dai Kungiyar tace Gwamnati
ba tayi komai ba.
Kungiyar tace kowace Makaranta tana cikin yajin, to sai dai ga shi
Makarantar Polythechnic ta Jihar Kaduna ba ta bi sahu ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment