Gwamnati
ta saki makudan Biliyoyi domin aikin jirgin kasa
Rahotanni daga Jaridar Punch
sun nuna cewa Gwamnatin tarayya ta saki kudi har Naira Biliyan 72 domin shirin
fara aikin jirgin kasa Legas zuwa Ibadan. Ministan sufuri na Kasar, Rotimi
Amaechi ya tabbatar da wannan jiya.
Minista Rotimi Amaechi yace
wannan yana cikin bangaren kudin da za ayi amfani da su wajen zamanantar da
hanyar jirgin kasar. Ministan yace aiki za a fara gadan-gadan ba tare da
wata-wata ba kuwa.
Wannan ne dai karo na farko
da aka fitar da irin wannan mahaukatan kudi domin wani aiki. Amaechi ya roki
Majalisar Kasar ta taimaka ta amince da rokon Shugaba Muhammadu Buhari na ciwo bashin dala
biliyan 30.
A taron Gwamnatin tarayya ta
fitar da wasu hanyoyi har guda 59 da za su fitar da Kasar daga halin da ake
ciki na matsin tattalin arziki. Minista Udo Udoma ya bayyana hakan, daga ciki
akwai dawo da akala kan abubuwan da ba su shafi man fetur ba irin su noma da
ma’adanai.
No comments:
Post a Comment