Gwamnoni sun shiga taitayin su
– Sakamakon abin da ya faru da
Gwamna Wike da Ayo Fayose, Gwamnoni sun shiga taitayin su
– Yanzu haka, Gwamnoni da dama sun
daina waya a salula gudun tonon silili
– Gwamnonin sun komawa kafafe irin
su Whatsapp da sauran su
Gwamnoni
dai sun yi wa kan su karatun ta-natsu bayan ganin abin da ya faru da ‘Yan uwan
su. Kwanan nan wani sabon sauti ya fito, inda aka ji Gwamna Fayose da Gwamna
Wike suna murnar murde zaben Jihar Ribas da suka yi.
Jaridar
Punch tace wannan dalili ya sa Gwamnoni da dama sun shiga taitayin su, sun kuwa
daina magana ta wayar salula muddin dai abin da za a tattauna din ba karamin
lamari bane. Hukumar DSS dai na daukar irin abin da Gwamnonin suka tattauna a
wayar tarho.
Gwamnonin
dai sun komawa kafafen sadarwa na zamani na yanar gizo irin su whatsapp da facebook da abin da ake kira BBM
domin isar da sakonnin su. Wasu daga cikin irin wadannan kafafe dai suna
bada daman zance na sirri da kuma hana wani bare ya dakile ko ya ga sakon da
aka aika.
A
baya-bayan nan dai, an dai samu sautin wayar tarhon da ya wakana tsakanin shi
Gwamna Fayose da takwaran sa, Wike na Jihar Ribas. Fayose yace wannan abin kunya
ne ace ana amfani da Hukumar DSS domin dauko tattaunawar su. An ce dai wani
Gwamna har ya nemi na’ura da ke bayyanawa mutum idan har ana leken sa. Wasu
kuma sun komawa irin tsofaffin wayoyin nan na da.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment