Monday, January 16, 2017

UEFA ta fitar da sunayen manyan masu masu horo na Duniya


– Kungiyar UEFA ta fitar da jerin kwararrun masu horaswa da babu irin su


– Babu sunan su Pep Guardiola na Kasar Spain


– Sir Alex da Jose Mourinho sun samu shiga





Kungiyar UEFA ta fitar da sunayen masu horaswan da ba a taba yin irin su ba a Duniya. An dai kafa Kungiyar ne a shekarar 1954. Kungiyar ta kunshi manyan zakaru na Nahiyar Turai a kwallon kafa.

Kocin da aka jero dai sun hada da: Sir Alex Ferguson wanda ya rike Kungiyar Manchester United ta Ingila ya kuma lashe Gasar har sau 2. Haka kuma jerin na dauke da sunan Jose Mourinho mai rike da Kungiyar ta Manchester wanda shi ma ya ci Kofin sau 2 tare da Kungiyar FC Porto da kuma Inter Milan.

Sauran wadanda suka shiga wannan sahu su ne: Brian Clough da ya ci wa Kungiyar Nottingham Forest ta Ingila wannan gasa har sau 2 shekarun baya can. Sannan Johan Cryuff wanda ya canza rawan Barcelona, Vincent Del Bosque na Kasar Spain, Helenio Herrera, Udo Lattek, Valeri Lobanovskiy, Rinus Michels da kuma Arigo Sacchi; wanda ya lashe Kofin na Uefa sau biyu a jere.

Sai dai irin su Arsene Wenger, Rafa Benitez, da Carlo Ancelotti, har ma Pep Guardiola ba su samu shiga cikin wannan jeringiya ba.




[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...