Monday, January 16, 2017

Farfesa Tanko ne sabon Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna



Jami’ar KASU: An nada sabon Shugaba




Jami’ar KASU ta Kaduna ta nada sabon Shugaba


Farfesa Mohammed Tanko ne sabon Shugaban Jami’ar


Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da nadin



A jiya ne Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya tabbatar da nadin Farfesa Mohammed Tanko a matsayin Shugaban Jami’ar ta Jihar Kaduna watau KASU. Wannan ya biyo bayan mataki da Hukumar kula da Jami’ar ta dauka

Farfesa Tanko dai Malamin Jami’ar ne tun asalin sa, ya rike Shugaban sashe da Tsangayan Tattali na Makarantar da kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar a baya. Kai bari ma dai ya taba rike Mukaddashn Shugaban Jami’ar a wani karo, don haka ya san harkar Jami’ar ciki-da-bai.

An haifi Mohammed Tanko ne a Kawo, Farfesa ne a bangaren akawu. Tanko yayi Digirin san a farko a Jami’ar Bayero ta Kano a fannin Ilmin akawu, daga nan yayi digirgir da kuma MBA a shekarar 2000. A shekarar 2005 Tanko ya kammala karatun Digiri na uku a Jami’ar ABU Zaria.

Farfesa Tanko kwararren Akawu ne, ya kuma rike matsayi da dama har a Gwamnatin Jihar Kaduna, ya kuma yaye dalibai masu karatun Digiri da dama. Yana da rubuce-rubuce masu yawan gaske.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...