– Sabon
shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya dawo gida
– Adama Barrow ya shigo Kasar sa
bayan Yahaya Jammeh ya fita
– Barrow ya baro Kasar Sanagal inda
ya labe
Sabon
shugaban Kasar Gambia da aka zaba a karshen bara, Adama Barrow ya taba Kasar
Gambia. A jiya ne Barrow ya shigo Garin Banjul na Kasar ta Gambia, bayan da shi
kuma Yahaya Jammeh ya bar Kasar.
Kamar
yadda BBC ta fada, Jama’a sun yi dafifi a filin jirgi inda suke jiran sabon
shugaban na su Adama Barrow ya iso. Barrow dai ya dade a labe a Kasar Senegal
tun bayan da aka zabe sa, kafin a rantsar da shi.
An
dai ga Sojojin Najeriya suna sintitiri yayin da Barrow ya shigo Kasar. Dakarun
ECOWAS dai suka matsawa Jammeh har sai da ya sauka daga mulkin bayan ya fadi
zabe, ba dan yana so ba. Jammeh ya fi shekaru 20 yana mulkin Kasar Gambia.
Da alamu dai tsohon Shugaban
Kasar Gambia, Yahaya Jammeh zai cigaba da rayuwar jin dadi ne ko a zaman gudun
hijirar da zai yi. An
dai bar Jammeh ya tafi da ingaramammun motocin har guda 13 zuwa Kasar
Equatorial Guinea inda zai yi zaman san a Gudun Hijira.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment