– Sanata Shehu Sani yace sam ba Shugaba Buhari ya rubuta wasikar da ta wanke Babachir ba
– A
wasikar da aka maido wa Sanatocin martani jiya, shugaban kasa ya wanke Babachir
Lawal
– Shehu
Sani yace an yi jana’izar yaki da rashawa
Sanata Shehu Sani mai
wakiltar Yankin tsakiyar Kaduna yayi tir tare da mamaki ga martanin wasikar da
aka samu daga fadar Shugaban kasa inda aka wanke Sakataren Gwamnatin Tarayya,
Babachir David Lawal daga dukkan zargi.
Shehu Sani yace Fadar
Shugaban Kasa tayi karya a wasikar ta, Sanatan yace ba shakka sun gayyaci
Sakataren Gwamnatin domin ya kare kan sa a Majalisar. Haka kuma Sanatan da ya
gudanar da bincike game da Sakataren yace kusan ‘yan kwamitin na sa, sun sa
hannu a takardar da ya gabatar ba kamar yadda wasikar Shugaban Kasa ta fada ba.
Shehu Sani dai yayi mamakin
yadda Fadar Shugaban Kasa tayi mursisi ta hau kujerar naki game da rokon da aka
yi na tsige Sakataren Gwamnati, Babachir David Lawal bisa zargin mikawa
Kamfanin sa wasu kwangila.
Shehu Sani yace yanzu an yi
jana’izar yaki da cin hanci da rashawa a Gwamnatin Shugaba Buhari. Don kuwa ana
tsince wadanda za a bincika ne da laifi a Mulkin na Buhari.
No comments:
Post a Comment