– Shugaban
kasar Gambia Yahaya
Jammeh ya kafa dokar ta baci
– A Ranar Alhamis wa’adin Shugaban Kasar ke cika
– Ministocin Gambia sun fara murabus
– Da sa hannun Majalisa
– Sojojin Najeriya za su shiga Kasar Gambia?
Yayin
da ake tsammani Adama Barrow ya zama sabon shugaban kasar Gambia, Shugaba
Jammeh da ke kan kujera ya kara nuna cewa ba sa da niyyar sauka. A Ranar Alhamis
dinnan ne dai wa’adin Jammeh ke karewa.
Sai
dai kwatsam aka ji sanarwar kafa dokar ta-baci a Kasar baki daya. Hakan ya biyo
bayan Ministocin Kasar da dama sun yi murabus. Tuni dai Ministocin tattalin
arziki, harkokin kasar waje da na kasuwanci da ma na Muhalli suka yi murabus
daga Gwamnatin.
Shugaba
Jammeh dai ya sanar da cewa an kafa dokar ta-baci, za kuma a dauki mataki na
watanni uku domin Kasashen wajen sun fara katsalandar a cikin harkokin Kasar.
Shugaba Jammeh yace hakan na iya kawo wa Kasar ta Gambia matsala.
A makon nan Shugaban Kasa Jammeh ya nemi
a dakatar da rantsar da sabon Shugaban Kasa Adama Barrow, sai dai Kotu ba ta
amince da hakan ba. Barrow ne ya lashe zaben da aka yi a watan jiya, wa’adin
shugaba Jammeh dai zai cika ne gobe, sai dai yace ba zai mika mulkin ba duk da ya fi shekaru 20 a kai.
Majalisar Kasar ce dai ta dauki matakin kafa dokar ta bacin bayan tayi wani zama a boye. Shugaba Jammeh dai ya roki Najeriya su rabu da Kasar Gambia. Da alamu dai dakarun Najeriya na shirin Kasar Gambia wanda karama ce kuma ba ta da wani karfin kirki.
.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment