– Fasto Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani
– Faston yace duk Makiyayin da
aka gani kusa da Cocin sa a aika sa Lahira
– Wannan kalaman dai suna iya kawo
rikici a Kasa
Wani
Fasto mai suna Johnson Sulaiman ya ba Mabiyan sa umarnin kashe duk wani
Makiyayi da aka gani kusa da Cocin sa. Babban Faston na Omega Fire yace idan
har aka ga wani Fulani-Makiyayi kusa da cocin sa, a aika sa Lahira kurum.
Faston
yace Makiyaya Fulanin suna neman kai masa hari su ga bayan sa. Yanzu haka dai
bidiyon na ta yawo a yanar gizo, ko da yake ba a san yaushe ne Faston ya fadi
wannan maganar ba, amma dai da alamu cikin ‘yan kwanakin nan ne.
Faston
dai yace Fulani Makiyaya suna kokarin tada fitina a Cocin na sa, yace don haka
ne wani ya kira sa ya fada masa domin ya dauki mataki. Don haka ne dai ya sanar
da Mabiyan sa cewa ka da a ragawa wani duk Makiyayi da aka gani a kusa da wurin
bautar na su.
Faston
yace ko da wasa wani Makiyayi ya shigo a yanka wuyan sa, a kashe shi, kuma babu
abin da zai faru. Wannan kalamai dai suna iya tada rikici.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment