– Yanzu haka da wannan sana’a yake
cin abinci
– Aliyu na zaune a Garin Kafanchan a Jihar Kaduna, yace gado yayi
– Aliyu Ahmed Kabir ya kammala karatun san a Digiri, amma ya koma harkar shayi da biredi
Wani Bawan Allah mai suna
Aliyu Ahmed Kabir ya dage da sana’ar sayar da shayi da Biredi bayan ya kuwa
kammala karatun sa na Jami’a. Yanzu haka Aliyu yana da Dan Teburin sa na shayi
a kan layin Bebeji da ke Kafanchan a cikin Kudancin Kaduna.
Aliyu ya karanta Ilmin
ma’adanai na karkashin kasa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta Bauchi tun a
shekarar 2013. Kafin nan ma Aliyu ya karanci abin da ya shafi kiwon lafiya a
wata Makarantar tsabta ta Jihar da ke Ningi.
Aliyu dai yace in dai shayi
ne, gado yayi. Kuma halin rashin aikin yi a Kasar ya sa ya cigaba da wannan
sana’a. Daridar Daily Trust tace Aliyu ya bayyana cewa ya kan yi dariya idan
har ya ga masu karatun diploma da shaidar NCE suna yanga wajen neman aiki,
Aliyu yace takardar shaida ba karan komai bace.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment