– Jami’an Hisbah sun fasa kwalaben
giya a Kano fiye da 1000
– Wannan a shekarar da ta gabata kurum kenan
– Dokar
shari’a ta haramta shigo da giya
Jami’an Hisbah a Kano sun
fasa kwalabe sama da 1000 na giya a Jihar Kano da a ka kama shekarar da ta
wuce. Darektan Hukumar Hisbah ta Jihar mai kula da harkokin Addinin Musulunci
ya bayyana haka ga manema labarai.
Abba Sufi yace Ma’aikatan
Karamar Hukumar Dawakin Kudu suka yi wannan aiki a Ranar Talatan da ta wuce. An
dai kona kwalaban ne a gaban Ma’aikatan Hukumar da sauran Jama’a. An karbe
kwalaban giyan ne bayan an bada hukunci a Kotu.
A Jihar Kano dai ana amfani
da dokar shari’ar Musulunci wanda ta hana shigowa ko shan kayan barasa.
Ma’aikatan Hisbah kuma za su kara kokari wajen ganin an bi wannan doka a fadin
Jihar a wannan shekarar da aka shiga.
A bangaren siyasa kuwa, ‘Yan
Kwankwasiyya a Jihar Kano sun yi kokarin gudanar da wani taro a Ranar Litinin
din wannan makon, sai dai abin bai yiwu ba, bayan da aka turo ‘Yan Sanda suka
zagaye wajen taron. Jaridar Daily Trust dai ta bada labarin abin da ya faru.
No comments:
Post a Comment