Tuesday, January 10, 2017

Mulkin Amurka ba mulkin gidan ka bane: Obama ga Trump


Ka bi a hankali, Obama ya gargadi Trump


Barrack Obama ya ba Donald Trump shawara yadda zai rike Kasar Amurka


Obama ya gargadi Trump da ya bi a hankali wajen mayar da Kasar kamar aikin Gidan sa


– Obama yace yanzu Trump zai gane shayi ruwa ne




Shugaban Kasar Amurka mai shirin barin gado Barrack Obama ya gargadi Sabon Shugaban Kasar-da aka zaba Donald Trump da ya bi ta ka tsan-tsan wajen mulkin Kasar. Obama ya ba Donald  Trump shawarar yadda ya kamata ya tafiyar da mulkin sa. Obama yace da Trump sha'anin Amurka ba irin na Gidan sa bane.

Shugaba Obama yace ya kamata Trump ya fahimci cewa Shugabancin Kasar Amurka ya sha bam-bam da na cikin gidan sa. Donald Trump dai bako ne a siyasa ko da dai hamshakin dan kasuwa ne. Obama yace su kan tattauna da Sabon Shugaban Kasan a ko yaushe. 


Gidan Talabijin na ABC ta rahoto Obama yana bayyanawa Trump cewa yanzu fa zai gane ana yin ta; don kuwa akwai matukar bambanci tsakanin yakin neman zabe da kuma Shugabancin Kasar. Obama dai yace shi da Trump kamar gabas da yamma suke wajen akida.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...