– Gwamnatin Jihar Katsina ta bada lamuni ga barayin dabbobi
– Tsofaffin
barayin shanun da dama sun mika wuya, sun ajiye makamai
– An maido bindigogi da dabbobi da dama
Gwamnatin Jihar Katsina ta
bada lamuni ga barayin dabbobi a Yankin. Hakan ta sa da dama sun ajiye makaman
su ga hukuma. An dai samu bindigogi fiye da 300 da kuma dabbobi masu yawan gaske.
Bayanai sun nuna cewa an
samu maido dabbobi sama da 28,000 da aka sata a baya. An dai kuma samu bindogin
AK har guda 97 da kuma sauran kananan bindigogi fiye da 200. Daruruwan mutane
ne dai suka mika wuya suka ajiye makaman na su yayin da Gwamnati ta bada
lamuni.
Sakataren Gwamnatin, Dr.
Mustafa Inuwa ya bayyana haka a Garin Kankara idan aka mika makaman. Wannan dai
yana cikin kokarin Gwamnatin na kawo karshen rikicin makiyaya da manoma. Tuni
dai an mika mafi yawan dabbobin da aka maido ga masu su.
A Kaduna kuma, Dan Majalisar
da ke wakiltar Karamar Hukumar Kaura da ke cikin Kudancin Jihar, Honarabul
Gideon Gwani ya koka da yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Yankin. Dan
Majalisar yace Mutanen suna cikin matsala dare da rana.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment