Tuesday, January 17, 2017

Kare ya kashe ‘Dan Shugaban Kasa


– Adama Barrow ya rasa ‘Dan sa bayan da kare ya gartsa masa cizo


– Habibu Barrow mai shekaru 8 a Duniya ya rasu


A na dai jira Ranar Alhamis tayi a ga ko za a rantsar da Barrow



Yayin da ake shirin ganin an rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambia, ya rasa daya daga cikin ‘ya ‘yan sa Habibu. Habibu ya rasu ne a Asibitin Manjai da ke kusa da Garin Banjul.

BBC ta rahoto cewa Habibu Barrow ya rasu ne bayan da wani kare ya gartsa masa cizo. Wannan ne dai yayi sanadiyar yaron mai shekaru 8 rak a Duniya. Tuni dai har an birne Habibu duk da Mahaifin na sa ba ya Kasar.



Adama Barrow ya tsere zuwa Kasar Senegal inda ya fake yana jiran ranar rantsarwa domin a nada sa sabon shugaban kasar Gambia. Habibu dai ya rasu ne shekaran jiya. Barrow yana da mata biyu da ‘ya ‘ya hudu.

Idan ba a manta ba Alkalin Alkalai na Kasar Gambia, Emmanuel Fagbenle ya ki amincewa da karar Yahaya Jammeh da Jam’iyyar sa ta APRC na cewa a dakatar da nadin Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasa. An dai nemi Alkalin ya kauracewa rantsarwar sabon Shugaban Kasar. 

Barrow ya ci zabe, amma kuma Jammeh yace fau-fau ba zai sauka daga kujerar ba. Ko ya za a kare kenan?



[NAIJ Hausa]






No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...