Monday, January 23, 2017

An soke rajistar Jaridar Al-Mizan


– Kungiyar ‘Yan Jarida na Kasa ta soke rajistar Jaridar Al-Mizan


– NUJ tace tayi kuskure wajen rajistar Jaridar


– Jaridar Al-Mizan ta ‘Yan Shi’a ce




Kungiyar NUJ ta ‘Yan Jaridun Najeriya ta soke rajistar Jaridar nan ta Al-Mizan. Wannan mataki dai ya zo ba da bata wani lokaci ba kamar yadda Kungiyar ta bayyana bayan wani taron da tayi a karshen makon da ya wuce.

Sakataren Bangaren Kungiyar na Jihar Kaduna, Dauda Idris Doka ya sa hannu wajen matakin da aka dauka. Kungiyar ta bayyana cewa ta gano Jaridar ta ‘Yan Shi’a ce a zaman ta da tayi na zartarwa a Ranar 29 ga watan nan.

Kungiyar ta NUJ dai tace ba ruwan ta da wani addini, asali ma dai tana kokarin kare duk wasu Addinai da kuma Kabilu na Kasar ne. Kungiyar don haka tace tayi kusukuren ba Jaridar Al-Mizan lasisi a baya. Daga yanzu dai bai hallata  Jaridar ta ci gaba da aiki ba.

Jaridar Al-Mizan din da kuma ta Turancin ta watau Pointer Express ta Kungiyar IMN ce ta Shi’a. A baya dai NUJ ta hana Jaridu da dama lasisi saboda wannan dalilai.





[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...