Tuesday, January 10, 2017

Rashin Albashi ya sa Ma’aikata sun koma azumi a Kwara



– A Jihar Kwara, Ma’aikata sun komawa Azumi da Salla bayan an yi wata da watanni babu albashi


– Gwamnatin Kwara dai ta kwashi watanni 6 ba ta biya Ma’aikata albashi ba



Yanzu haka a Garin Ilorin, Malaman Makaranta da dama sun koma azumi inda suke rokon Ubangiji ko a samu a biya su albashin sun a wata-da-watanni. Ma’aikatan Makaranta na bin Gwamnatin Jihar Kwara dai bashin albashi har na watanni 6.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Malamai watau NUT ya bayyana haka a Ranar Litinin. Alhaji Salihu Toyin wanda shine kuma Shugaban wata Makaranta a Ilorin yace yanzu kuma sun koma hannun Ubangiji ko albashin su zai fito.

Jaridar Vanguard tace, Yanzu dai Malaman Makaratun Jihar za su shiga azumi da rokon Ubangiji da Musulman su da Kirista domin su samu kudin su. Gwamnati dai ta fara biyan wasu albashin, amma har yanzu Ma’aikatan na bin bashin wasu kudin. Malaman Makarantun Kwara dai suna shan wahala matuka.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...