Monday, January 2, 2017

Gwamnati za ta saye Injin Janareto na Biliyan 8



Yayin da ake sa ran wuta ta gyaru, Gwamnati ta shiryawa sayen Janareta shekarar nan


An yi kasafin sama da Naira Biliyan 8 domin sayen Injin ba-da wuta


Ana dai fama da karancin wuta a Kasar nan




Gwamnatin tarayya ta shirya sayen Injin ba-da wuta na kudi har sama da Naira Biliyan 8 a wannan shekarar. Wannan kudi da Gwamnati tayi kasafi za a ware su ne kawai domin sayen sababbin Injin wuta da kuma gyara wadanda ake da su a Kasa.

Gwamnatin dai ta ware Biliyan 8.4 domin Injin janarato kawai a kasafin kudin shekarar bana. Za a kashe kusan Biliyan 2 wajen gyaran wasu Injin, sannan za a kashe fiye da wasu Biliyan 2 wajen sayen sababbi. Za kuma a kashe ragowar kudin wajen sayen mai.

Cikin dai wadanda za su fi kowa amfani da Injin ba-da wutar sune Ma’aikatar wuta da kan ta na Kasar. Sauran Ma’ikatu irin na Kudi da Kasuwanci na Kasar, su ma ba a bar su a baya ba. Filin Jirgin Shugaban Kasa ma dai zai ci sama da Miliyan 30 wajen man Janareta.

A dai kasafin kudin bana na sama da Naira Tiriliyan 7, ana sa ran Fadar Shugaban Kasa za ta kashe makudan kudi wajen sayen cokula da ludayi na cin abinci.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...