Bai dace Ayo Fayose ya jagoranci
PDP ba-Inji Sanata Kashamu
– Sanata Buruji Kashamu yayi raga-raga da Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti
– Sanatan yace bai dace a nada Ayo
Fayose a matsayin Shugaban Gwamnonin PDP ba
– Makon jiya aka nada Gwamna Fayose a matsayin
Shugaban Gwamonin PDP na Kasar
Sanata
Buruji Kashamu yayi tir da shawarar da Jam’iyyar PDP ta dauka na nada Gwamna
Ayodele Fayose na Jihar Ekiti a matsayin shugaban Gwamnonin Jam’iyyar PDP.
Fayose dai ya canji Gwamna Mimiko wanda wa’adin sa na daf da karewa.
Buruji
Kashamu Sanata mai wakiltar Gabashin Ogun yace ko kadan Fayose bai dace da
rikon wannan shugabanci ba. Kashamu yace hayaniya kurum ya cika kan na Fayose,
babu ilmin komai. Kashamu ya kara da cewa Fayose yak an yi abubuwa kamar
karamin yaro, yace da irin su aka nada a wannan matsayi.
Buruji
Kashamu yace ya kamata ‘Yan PDP su nuna rashin amincewar su da wannan mataki da
aka dauka. Kashamu yace babu abin da Fayose zai yi illa ya kashe Jam’iyyar PDP
gaba daya don kuwa babu wanda zai yi aiki da shi.
No comments:
Post a Comment