Madalla:
Farashin gangan man fetur yayi sama
– Farashin gangan man fetur ya lula sama
–
Fiye da shekara guda kenan rabon da kudin gangar mai ya kai haka kudi
– Sai
dai shin za a dore a haka?
Farashin gangar mai a Duniya
ya daga sama fiye da yadda aka sa rai. Rabon da man fetur yayi wannan kudi dai
tun Watan Yuli 2015. Jaridar Bloomberg dai ta bayyana haka tana kuma mai
shakkan ko farashin zai dore a haka.
Yanzu haka dai kusan kudin
gangan mai ya kai Dala $58.37 a farkon shekarar nan. Hakan dai ya yiwu ne bayan
an cin ma wata yarjejeniya tsakanin Kasashen OPEC da wadanda ba su cikin
Kungiyar OPEC din.
Kasashe irin su Kuwait sun
amince su rage yawan man fetur din da suke hakowa a Kasa a kullum. An dai shuga
sabuwar shekara da labara mai dadi, musamman a Kasashe irin su Najeriya da suka
dogara da kudin mai.
Haka kuma har wa yau
Kamfanin mai na Kasa watau NNPC ya fitar da jeringiyar sunayen Kamfunan da aka
ba damar shigo da mai cikin Kasar nan wannan shekarar. A ciki akwai Kamfunan
‘Yan Kasuwar Najeriya guda irin su Wale Tinubu da kuma A.A Rano.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment