Sunday, January 15, 2017

Za mu tunbuke Jammeh da karfin tsiya-ECOWAS




– Kungiyar ECOWAS na shirin tunbuke Shugaban Kasar Gambia Yahaya Jammeh


– ECOWAS tace ta tanadi Sojojin da za su kutsa Gambia domin ganin bayan Jammeh ko babu girma, ba arziki


Shugaban Kasar ya fadi zabe, ya kuma ce ba zai sauka ba





Rikicin siyasar Kasar Gambia na ta kara cabewa bayan da Kungiyar ECOWAS ya Kasashen Afrika ta Yamma ta ce za ta cire Shugaban Kasar Gambia ko ya ki-ko ya so. ECOWAS tace ta shirya Rundunar Soji da suka shirya tunbuke Yahaya Jammeh.

Yanzu haka dai Shugaba Buhari ya taka har Kasar, inda ya zarce zuwa Mali domin ganin Shugaban Kasar na Gambia ya sauka daga mulki bayan ya sha kayi a zabe. Kasashen sashin Nahiyar dai suna shirin hada Runduna domin tinkarar Kasar Gambia da Shugaban Kasa Jammeh.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Kasashen na Afrika na neman izini daga Majalisar dinkin Duniya domin far wa Kasar ta Gambia, ba girma ba arziki. Wani Manzo na Majalisar Dinkin Duniyar, Muhammad Ibn Chambas yace ko ta halin kaka sai an sauke Jammeh an daura Adama Barrowa wanda ya lashe zabe.

Kwanakin baya ne Shugaban Kasar Gambia ya sanar a Gidan Talabiji cewa ba abin da zai sa ya sauka daga Shugabancin Kasar bayan shekaru fiye da 20 yana kai. Ya dai sha kashi a zaben takarar da aka yi a bara.




[A duba shafin NAIJ Hausa domin samun labarai da dumi-dumi]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...