– Majalisar Dattawa ta nemi a kara duba maganar haramta shigo da motoci ta Kasa
– Yanzu babu damar shigo da motoci sai ta iyakar teku
– Majalisa ta nemi a saba wannan doka
Karshen shekarar can ne
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin Kasar
nan ta iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da
tsofaffin motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya kamar yadda Hukumar Kwastam ta
sanar.
Sai dai Majalisar Dattawar
Kasar tace ba ta aminta da wannan ba. Majalisar tace yin hakan zai sa mutane
sama da 500,000 su rasa aikin yi. Sanatocin Kasar sun ce wannan doka ba za ta
taimaki talaka ba.
Sanata Barau Jibril na Jihar
Kano ya kawo wannan kudiri, Danuwan sa Sanata Kabiru Gaya ya mara masa baya a
kan haka. Haka nan sauran Sanatoci irin su Sanata Shehu Sani sun yi fata-fata
da wannan doka.
Sanotocin sun kuma nemi a janye wannan doka cikin gaggawa. Majalisar dai ta kuma nemi ayi bincike game da batun tare da rokon Shugaban Kasa ya ji kukan Jama’a ya janye
dokar.
No comments:
Post a Comment