DSS ta damke wani Dan Boko Haram a
Kaduna
– Jami’an tsaro sun sun damke wani ‘Dan Boko Haram a Garin Kaduna
– Hukumar DSS ta damke ‘Yan
ta’addan a Kaduna bayan sun gudo daga Jihar Yobe
– DSS tana samun nasara wajen
kama ‘Yan Boko Haram da suke cikin Garuruwa
Hukumar
DSS tayi namijin kokari bayan da ta damke wani Dan Boko Haram da ke shirin kai
hari a cikin Garin Kaduna. Dan Boko Haram din dai ya tsero ne daga Jihar Yobe
da niyyar tada kayar-baya a Garin na Kaduna.
Jami’an
Tsaro na DSS dai sun yi nasarar kama wannan Dan Boko Haram kafin yayi ta’asa.
Jami’in Hukumar Tony Opuiyo yace sun kama wani Dan Boko Haram mai suna Alkassim
Salisu wanda ya shirya kai hari a cikin Kaduna.
‘Yan
Boko Haram da dama sun tsero daga Yankin Arewa maso Gabashin Kasar bayan da
Sojojin suka fatattako su. Maimakon wannan ya nemi zama lafiya, sai ya ma kuma
fara shirin yadda zai kawo wani sabon rikici.
Hukumar
DSS din suna cigaba da damke ‘Yan Boko Haram da sauran masu laifi a cikin
Kasar. Hukumar tace tayi nasarar damke masu laifuffuka da dama a cikin Kasar;
daga masu garkuwa da mutane zuwa ‘Yan ta’adda a Garin Fatakwal, Taraba, Kogi,
Legas, Kano, dsr.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment