Tuesday, January 17, 2017

‘Yan Kudancin Kaduna suna neman a basu Jiha


An fara fafatukan neman Jihar Kudancin Kaduna


Yankin dai na ta fama da rikici dabam-dabam


Wani Fasto ya nemi Shugaban Kasa ya zamar da Yankin Jiha mai zaman kan-ta



Masu kira sun fara kira da a ba Yankin Kudancin Kaduna Jiha mai cin gashin-kan ta. Sakataren Kungiyar Fentakwastal ta Kiristocin Najeriya Emmanuel Nuhu Kure ya fara wannan kira. Rikivin Yankin ya sa Faston yayi wannan kira.

Sakataren na Kungiyar PFN yace ya dace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mayar da Yankin Kudancin Kaduna ta zama Jiha mai zaman kan ta. Kure yace idan har aka yi hakan, za a yi maganin rikicin da ake tayi tsakanin Fulani Makiyaya da mazauna Yankin.

Fasto Emmanuel ya bayyana haka ne ga manema labarai a wata magana da aka yi da shi a wayar tarho. Fasto Emmanuel Nuhu Kure yace idan neman zaman lafiya kurum a ba Mutanen Yankin Jiha guda, yace ko dama can duk Kiristoci ne.

Kwanan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugabannin Hafsun Sojojin Kasar nan wajen ganin kawo karshen rikicin Kudancin Jihar Kaduna  da sauran Yankuna da ake tada rikici irin su Neja-Delta. Faston ya yabawa Shugaban Kasar da wannan kokari.



[NAIJ Hausa] 







No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...