–
Sabon Shugaban Kasar Amurka zai fuskanci kalubale game da sababbin tsare-tsaren sa
– Tuni Kasashen Duniya sun fara nuna Trump da
karamin yatsa
– Ko za a kwashe da Trump lafiya kuwa?
Idan ana bin labarai dai an san cewa a Ranar Juma’ar da ta gabata ne, Shugaban Kasar Amurka
Donald Trump ya nemi a hana baki da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar
Amurka. Trump ya nemi ya
hana Kasashe 7 na Musulmai shiga cikin Kasar.
Sai dai Jama’a da dama sun soki wannan tsari, suna ganin ba zai yi wani
tasirin kirki ba, wasu ma suna ganin cewa akwai munafunci a tsarin na Trump.
Mutanen Amurka sun ta buga zanga-zanga, daga baya kuma aka samu wata Kotu ta
bada umarnin dakatar da tsarin na Trump. Bugu da kari ma dai Shugaba Trump din
ya kori Atoni-Janar na Kasar bayan ta ki kare tsarin na sa na korar baki.
A Jiya ma dai Tsohon Shugaban Kasar, Barrack Obama yace sam bai yarda da
wannan tsari na Trump ba, ko ta kusa ko ta nesa. Kwanan nan ne dai wani Tsohon
Dan wasa Mo Farah ya soki Shugaban Kasar da wannan manufar.
A baya dai Sanatoci da ‘Yan Majalisun Kasar na Jam’iyyar Democrats sun nemi
zama domin nuna adawar su da wannan doka. Dama wasu dai na ganin cewa daga
karshe dai tsige Donald Trump din za ayi tun kafin ya je ko ina.
No comments:
Post a Comment