– A jiya ne aka dasa wani bam a Masallaci cikin Jami’ar Maiduguri
–
Cikin wadanda suka rasu har da wani babban Farfesa
– Mutane
kusan 3 ne kuma suka rasa rayukan su
A jiya da Asuba ne dai aka
kai wani hari na kunar bakin wake a Masallacin Jami’ar UNIMAID ta Maiduguri. An
yi rashin sa’a mutane sun rasu, ciki har da wani babban Farfesa na likitan
dabbobi mai suna Aliyu Usman Mani.
Farfesa Aliyu Mani yana da
kusan shekaru 60 a Duniya, kuma shi ke rike da Asibitin koyon aiki likitam
dabbobi na Jami’ar. An haifi Marigayi Aliyu ne a Katsina inda yayi Firamare,
kana ya taho Makarantar Sakandare da ta share fagen shiga Jami’a a Kaduna a cikin
shekarun 1971 zuwa 1976.
Marigayi Aliyu Usman Mani ya
shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya koyi harkar likitan dabbobi, ya
kuma kammala a shekarar 1981. A shekarar 1982 ya fara koyarwa a Jami’ar ta
Maiduguri, bayan nan kuma yayi Digiri na biyu da na uku a Kasar Ingila.
Farfesa Aliyu Mani ya rike
Mataimakin tsangayar ta koyar da likitan dabbobi, kuma shine Shugaban Asibitin
koyar da likitan dabobbin kafin ya rasu jiya. Ya rasu ya bar ‘Ya ‘ya biyu a
Duniya.
Shugaban Jami'ar dai ya ce ba za a
rufe Makarantar saboda wannan harin ba. Kungiyar ASUU ta Malaman Jami'a tuni ta
dakatar da taron da za tayi.
Allah ya jikan sa
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment