Thursday, January 19, 2017

Za a kara farashin man fetur ne?


NNPC tayi magana game da rade-radin karin farashin man fetur


Kamfanin NNPC tace ba za ta kara farashin man fetur ba


Kwanaki Gwamnatin Shugaba Buhari ta cire tallafin man fetur




Kamfanin NNPC na mai na Kasa ta yi magana game da rade-radin da ake tayi na cewa za a kara kudin fetur a Kasar. NNPC tace babu maganar karin farashin man na fetur kamar yadda Jama’a ke fada.

Haka kuma NNPC sun yi kira da Jama’a su kwantar da hankalin su domin kuwa akwai mai a kasa. Jama’a dai na ta sayen dinbin mai suna ajiyewa gudun matsala nan gaba. NNPC dai tace tana da sama da lita biliyan daya na mai ajiye.

NNPC dai sun ce man da take da shi a ajiye zai isa Najeriya har na fiye da wata guda. Matatar man Najeriya duk sun fara aiki don haka babu maganar a samu karancin kanaziri ko man babbar mota. Wani Babban Jami’in NNPC, Mista Anibor Kragha ya bayyana haka da yake magana a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yace nan da ‘Yan shekaru mai zai zama ba komai ba a Duniya. Osinbajo ya kai ziyara Neja-Delta inda Gwamnati ke kokarin kawo karshen rikicin Yankin.
.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...