Tuesday, January 24, 2017

Watakila yau a tabbatar da Magu



‘Yan Majalisun Kasar nan na shirin fara zama domin kasafin kudin wannan shekarar


Majalisar Dattawa za ta fara zama game da kundin kasafin kudi


Watakila yau Majalisar Dattawar ta tabbatar da Magu





Rahotanni daga Jaridar Daily Trust na nuna cewa yau Majalisar Dattawa za ta fara zama domin ta tattauna abin da ya shafi kundin kasafin wannan shekarar. Sanata Baba Garbai Kaka  wanda shine Shugaban Kwamitin irin wannan al’amura ya bayyana haka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban Majalisar a karshen shekarar bara. Sai dai Majalisar ba ta ce komai ba tukun game da kundin har yanzu. Majalisar dai kwanaki tace tana da ayyuka da dama a gaban ta kamar su maganar rikicin Kudancin Kaduna da kuma haramta shigo da motoci, ga kuma kudirin PIB na bangaren mai.

Idan ba a manta ba kwanakin bayan ne Majalisar ta karkare batun takardun MTEF da kuma FSP da Shugaban Kasa ya kawo a baya. Zuwa wannan makon dai Sanatocin Kasar za su shiga tattauna game da kasafin bana wanda ya zarce Naira Tiriliyan 7.

Har wa yau kuma ana sa ran yau Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya kara karanto takardar shugaban kasa da ya ke nema a tabattar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC. A kwanakin baya dai Majalisa ta kora Ibrahim Magu bisa wasu dalilai.





[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...