Wani mutumi ya maida babur helikwafta
– Sai ga mota mai kafafu uku ta zama Jirgin sama
– Wani mutumi ya mayar da keke napep Jirgin yawo a Delta
– Abin mamaki dai da yawa yake
A
Kasar Warri watau Jihar Deltan Najeriya wani Mutumi mai basirar jaraba, ya
maida Babur dinnan da ake kira Keke Napep
mai kafafu uku jirgin saman helikwafta. Wannan
mutumi dai da hannun sa yayi wannan aiki, hakan ta sa har an fara kiran
Gwamnati ta agaza masa.
Wani
daga cikin wadanda abin ya burge sa yace sai dai babu abin da za ayi illa a
buga sunayen su a Jarida a tallata, bayan lokaci kadan kuma shikenan an manta
da su a Duniya. Wani ma dai da ya ga irin wannan abin a-zo-a-gani sai yace
aikin banza ne kurum da bata lokaci a wofi.
A
Najeriya dai Gwamnati ba ta maida hankali kan irin wannan yara da mutane masu
basira ba. Da a Kasashen waje ne sai a ba Mutum duk kwarin gwiwan da yake
bukata. A Najeriya kuma gara ma Mutum ya shiga wake-waken zamani ko wasan kwaikwayo.
A
wata Kasar kuma can wani Jaki ne kurum da ya gaji da daukar kaya, sai ya shige
cikin dawakai ya saje abin sa. Wannan abu dai ya ba mutane da dama mamaki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment