– A Ranar 15 ga Watan Junairun
kowace shekara ne ake tunawa da Sojojin Kasar nan
– A wannan Ranar ne aka kifar
da Gwamnati karo na farko a Kasar
– Haka kuma a Ranar 15 ga
Watan Junairu aka karbi Sojojin Yakin basasa
A
Rana irin ta Jiya ake tunawa da Sojojin Kasar da su ka riga mu kwanta dama. A
Ranar tunawa da Sojojin wannan shekarar ne Shugaba Buhari ya tura Bukola Saraki
ya wakilce sa a wani taron da aka yi a Abuja.
Shugaba
Buhari yayi magana da Sojojin Kasar da ke filin daga aka kuma yi ta’aziya ga
wadanda suka rasu. A dai Rana irin wannan ne aka kifar da Gwamnatin farko na
Kasar; aka kashe su Shugaba Tafawa Balewa da su Sardauna Ahmadu Bello. A juyin
mulkin ne manyan Sojojin Arewa irin su Laftana Pam, Laftana Largema, Kanal Kur,
da Birgdiya Maimalari suka tafi lahira.
A
kuma Rana irin ta haka ne ake tunawa da Sojojiin da aka karba daga Biyafara
bayan sun shiga Yakin basasa. An dai yi shekaru fiye da biyu ana gwabzawa inda
‘Yan Biyafara suke nemi su rabe daga Kasar.
Daya
daga cikin ‘Ya ‘yan Marigayi Laftana Pam, Dakta Ishaku Chollom Pam ya
bayyana yadda aka kashe Mahaifin sa a Juyi mulkin da aka yi a shekarar 1966.
Major Nzeogwu Kaduna ne ya jagoranci wannan juyin mulki da aka yi wa mafi
yawancin manyan Arewa kisan gilla.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment