– Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta mamayi wasu Yara da
ke Makarantar Katolika ta Kirista
– Uwargidan Shugaban Kasar ta yi alkawarin samawa Yaran
Makarantar ilmi mai nagarta
– Matar
Shugaban Kasan ta rabawa ‘Yan Makarantar kayan abinci
Matar Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bada gudumuwar kayan abinci ga Yara
kusan 300 da ba su da Gida. Matar Shugaban Kasar dai ta bada wannan gudumuwa ne
a Makarantar Katolika ta Paraxis.
Misis Paul Tallen, Tsohuwar
Matainakiyar Gwamnan Jihar Plateau ta wakilci Matar Shugaban Kasar inda aka
rabawa wadannan kayayyaki. Mai Makarantar, Mista Ben Onwudinjo ya tabbatar da
wannan abin alheri daga Hajiya Aisha Buhari.
Hukumar Dillacin labarai na
Kasa watau NAN tace Matar Shugaban Kasar tayi alkwarin samawa wadannan Dalibai
na Makarantar Paraxis na Katolika ta Addinin Kirista nagartaccen Ilmi. Tuni ma
dai har an sauyawa Makarantar suna zuwa Makarantar Hajiya Aisha Buhari.
A jiya kuma muka samu
labarin Uwargidan Gwamnan Jihar Ekiti, Feyisetan Fayose ta nemi Ubangiji ya
kare Mijin ta ya kuma tona asirin makiyan sa. Matar Gwamnan tace akwai masu
rabar Mijin ta alhali kuma ba masoyan sa bane na hakika.
No comments:
Post a Comment