BBOG
ku zo mu shiga Sambisa da ku-Gwamnatin Najeriya
– Gwamnatin Najeriya sun gayyaci ‘Yan Kungiyar BBOG zuwa ceto ‘Yan matan nan na Chibok
– Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ya gayyaci
‘Ya Kungiyar a wata wasika
– Ministan
ya nemi ‘Yan Kungiyar su aika Mutane 3 domin a shiga Dajin Sambisa da su
Gwamnatin tarayya ta
Najeriya ta Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ya gayyaci ‘Ya Kungiyar nan
ta BBOG watau BringBackOurGirls zuwa ceto ragowar ‘Yan matan nan da aka sace
shekarun baya a Garin Chibok.
Ministan ya nemi ‘Yan
Kungiyar su tura Mutane 3 domin a shiga Dajin Sambisa da su domin su ganewa
idanun su irin aikin da Sojin Kasar ke yi. Ministan ya aika wannan wasika ne
inda yake jinjinwa ‘Yan Kungiyar da kokarin na ganin an ceto ‘Yan matan na
Chibok.
Cikin wadanda za su shiga
wannan aiki akwai Shugaban Hafsun Sojojin sama na Kasar da kan sa da shi
Ministan da kuma Ministan tsaro na Kasar. Sai dai anya kuwa ‘Yan Kungiyar za su
amsa wannan goron gayyata na ceto ‘Yan matan da suka yi kwana 1000 suna tattaki
a kan su?
'Yan Kungiyar na BBOG dai sun bada wasu sharudda kafin su amince da wannan tayi. Madam Oby Ezekwensili ta bayyana cewa har sai an nemi afuwan su a kan wani kaifi da aka yi masu a baya kafin su karbi wannan tayi.
[Daga NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment