Wakar Ta'aziyyar Sardauna ta Marigayi Dakta Mamman Shata Katsina
Malam Ahmadu
Bello
Mujaddadi jikan
Mujaddadi Usmanu
Malam Ahmadu
Bello
Da farko
mun kuka,
Karshe mun ka yi
murna
Kayi gudu domin
abokan gaba.. Allah gwanda Shahada
Ahmadu gwanda
shahada
Kamar Ahmadu
Bello ace yayi gudu domin abokan gaba nasa.. Allah gwanda Shahada
Kamar Ahmadu
Bello ace yayi gudu domin abokan gaba nasa.. Mamman gwanda Shahada
Mai daraja
Ahmadu Bello
Mai daraja
Ahmadu Namu
Tun duniya ya
samo lahira
Malam Ahmadu
Bello
Musulmi na murna
Hausawa na murna
Hada har mara
hausa kowa na murna da halin Ahmadu Bello
Ga sada zumunci
Ga gyaran addini
Wurin Ahmadu
Bello
Kokari Ahmadu
Bello
Idan duk ka ga
ya raba yaje sai dai sada zumuci...
Sai gyaran
addini
Wurin Ahmadu
Bello
Mutum ne shi
muhimmi…
Mai son alheri…
Mai son zumunci
Ga sada zumunci
Sannan ga alheri
Sannan ga addini
Kana da baiwa
Kana da kyauta
Ahmadu Bello
Karshe mazajen
baya, ku nake shaidawa halin Ahmadu Bello
Arewar mu ta
farko
Arewar mu ta
Karshe
Kowane ya zama
daidai zamanin Ahmadu Bello
Kowane na Jin
dadi zamanin Ahmadu Bello
Allah ya jikan
Gamji!!!
No comments:
Post a Comment