HUDUBAR
JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA
Rayuwar Duniya-Daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar
A’udhu BilLahi minasshaidan
Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman
Ar-Raheem,
Dukkan Godiya sun tabbata ga
Allah, shi ne wanda ya hallaci Dan Adam daga yunbu, sannan ya zartar da ajalin
kowane daga cikin mu. Godiya da yabo sun tabbata gare shi Madaukakin Sarki, shi
ne wanda ya hallaci mutuwa da kuma rayuwa domin ya jarraba mu. Muna shaidawa
lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah, Shi kadai yake, babu abokin
tarayya a gare sa. Ya hallici Dan Adam daga turbuya, sannan kuma daga ruwan
maniyyi, haka nan kuma ya daidaita sa a matsayin Mutum. Muna shaidawa lallai
Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne. Allah yayi
alkwari ga duk wanda ya yarda da shi, ya kuma yi aiki na gari cewa zai ba sa
Aljanna ta Firdausi a matsayin Masaukin sa.
Bayan Haka:
Allah ya sanya bibiyar Dare
Da Rana su zama aya daga cikin ayoyi masu nuna cikar Ubangiji da nufin sa. Don
haka ne Allah yake fadi da Kan sa, Yake cewa: Shi ne wanda ya sanya Dare da
Rana ma su bin juna. Wannan ya kamata ya zama abin lura ga duk mai tunani mai
kuma so ya godewa Ubangijin sa. Ya kamata a gane cewa yadda wakanar Dare da
Rana su ke, haka rayuwar ma mai wucewa ce; watau abin da yake iyankatacce ne.
Ya kamata kowa ya ci moriyar wunin sa wajen abin da ya ke mai amfani. Kuma
Mutum ya kamata kullum ya zama yana tunanin aiki domin lahira. Shi dai lokaci
yana da muhimmanci a mizanin Musulunci matuka, Ubangiji SWT Yayi rantsuwa da
zamani a cikin Al-Qur’ani. Lallai Dan
Adam yana cikin asara face wanda yayi hakuri, kuma suka rikawa juna nasiha da
hakuri da juriya domin Allah… Saboda haka mai hankali shine wanda yake yi
wa kan sa hisabi yana lizamtar aiki na gari da kuma nisantar aiki na banza a
kowane lokaci. Shi dai mai hankali ya kan halarto da ajalin sa, yana tunawa
cewa akwai yiuwuwar ajalin sa na nan kusa. Ta hakane Mutum zai samu yardan
Allah tare da amfanar Mutane da kuma Jama’ar Kasar sa baki daya. Wannan dai shi
ne Mumunin da Annabi SAW yake bayani da yake cewa Mumuni ya kan zama yana aiki
domin gaba, mutuwa. Ai mafi yawa za a waye gari da Mutum, sai dai ba da shi za
a wuni ba, haka nan za a kwanta tare da Mutum, sai ya zama ba a wayi gari da
shi ba. Mafi yawa, sai ka ga mai burin kai gobe bai samu kaiwa ba. Allah SWT
dai yace ba ya jinkirta ajali idan har ya zo.
Ya kai Danuwa ko ‘Yar uwa mu
sani cewa lokacin da aka diba mana a Duniya, komai tsawon sa gajere ne. Saboda
haka bai kamata mu shagaltu da wani abu ba, har mu kasa morewa damar da aka
bamu. Za dai a tambaye kowane daga cikin mu game da wannan al’amari. Manzon
Allah SAW yace: Ranar tashin Kiyama, kafafun Mutum ba za su gushe ba har sai an
tambaye sa a kan abubuwan da yayi a rayuwar sa; ina kayi amfani da ilmin ka?
Ina ka samu kuma ka kashe dukiyar ka? Jikin ka, A ina ya tsofe???
Ya ku ‘Yan uwa idan har ku
na kokarin lissafi, idan har za a kasa yini zuwa uku, mafi yawan Mutane na
amfani da sa’a 8 wajen barci, suna kuma amfani da daya bisa uku wajen cin
abinci, kai-kawo, ziyara,Salloli, dsr. A kan batar da kuma ragowar lokacin
watau sa’a 8 wajen aiki ko sana’a. Watau dai da ace Mutum zai rayu shekara 60
bayan balagar sa; ya zama yayi barcin shekaru 20 kenan a rayuwar sa da kuma
shekaru 20 yana aiki. Mutum dai zai batar da shekaru 10 yana cin abinci, a
ragowar shekaru 10 ne Mutum zai zama yayi Salloli da sauran su. Yana dai daga
cin asara ya zama Mutum ya rayu ba tare da yayi wani aikin da zai taimaka sa a
lahira ba. An tambayi Manzon Allah SAW: aka ce a cikin Mutane wanene mafifici?
Ya ce wanda rayuwar sa tayi tsawo, ayyukan sa su ka yawaita.
Dan uwa kayi bakin kokarin
ka wajen aikin ka; ya zama aikin Gwamnati ko na Kamfani ko wata sana’a. Mutum
ya takarkare yayi aiki ba tare da ha’inci ba ko cin amana domin ka da lokacin
ka su tafi a banza. Ta hakane Mutum zai zama bai yi asarar lokacin sa a banza
ba, alhali kuma ya taimaki al’ummar sa. Allah SWT yana fada a cikin Al-Kur’ani
cewa ka fada masu ya Manzon Allah SAW cewa ku cigaba da aikin da kuke yi domin
Allah SWT da Manzon sa da Muminai za su gani, Shi Allah SWT a karshe zai bada
labarin abin da kuke aikatawa.
Allah ka ba mu fahimtar
Addini tare da zama lafiya. Allah ya karba mana ya tseratar da mu daga wuta.
Allah ka sa albarka cikin lokutan mu.
Ameen.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment