Wednesday, January 11, 2017

Abin da ya sa suka tsige ni-Sanata Ndume


Don nace ayi gaskiya suka tunbuke ni-Ndume




– Sanata Ali Ndume ya bayyana dalilin da ya sa aka tunbuke sa daga kujerar sa


– Majalisar Dattawa na Kasar ta cire Sanata Ali Ndume daga matsayin sa jiya


– Ashe a dalilin Magu ne aka cire Ndume


Sanata Ali Ndume ya bayyana zunubin da ya aikata da har ta sa aka cire sa daga Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawar Kasar. A jiya ne dai Shugaban Majalisa, Bukola Saraki ya karanta wata takarda daga ‘Yan APC mai nuna cewa sun cire Sanata Ndume daga matsayin sa.

Ali Ndume yayi wata hira da Jaridar Premium Times inda ya bayyana dalilin da ya sa aka cire sa. Ndume yace don ya nemi Majalisa ta yi gaskiya wajen tantance Ibrahim Magu na EFCC shiyasa aka sauke sa. Tun daga nan ‘ya ‘yan Jam’iyya suka fara kokarin juya masa baya.

Ndume yace ba a bi matakan da suka dace wajen kin tabbatar da Magu ba a matsayin Shugaban EFCC. Sanatan yace ba a bada dama domin ya wanke kan sa ba, sai dai kurum aka bayyana cewa Majalisar ba ta aminta da shi ba. Ndume yace kus-kus kawai aka yi wajen tabbatar da Magu, daukacin Majalisa ba ta zauna ba.

Dama can ana ta samun wasu bayanai masu cin-karo da juna a Majalisar. Sanata David Ummaru yace sam ba a tattauna maganar tantance Magu ba ko rashin hakan a zaman Majalisar. Sanata Ummaru dai shi ne Shugaban Kwamitin shari’a na Majalisar Dattawar Kasar.

Kafin dai Ahmed Lawan ya je yayi Sallah ya dawo, sai dai ya ji labarin har an tsige sa daga matsayin. Yanzu haka muna samun labarin cewa Jam'iyyar APC tayi na'am da wannan abu. Tuni dai an nada Ahmed Lawan a matsayin wanda zai maye gurbin na sa. Sanata Marafa yace saura kuma kujerar Ikweremadu



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...