– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya fara koro bakaken Afrika da suka tare Amurka gida
– Trump
ya sa kafar wando daya da bakin haure
– Donald
Trump kuma ya fara shirin gina katangar karfe tsakanin sa da makwabta
Sabon shugaban Kasar Amruka, Donald Trump ya sha
alwashin kare kaimi wajen bakin iyakokin Kasar Amurka saboda masu shigowa su
tare a Kasar ba a san da su ba. Yanzu haka dai har Trump ya fatattako ‘Yan
Afrika kusa 100 gida.
A Ranar Laraba ta Jiya sabon shugaban Kasar ya
fatattako bakin haure a Kasar har guda 92. A Ranar ne kuma Shugaba Trump din ya fara shirin
gina katangar karfe tsakanin Kasar Amurka da makwabta Kasar Mexico.
Cikin wanda Trump ya koro
akwai mutanen Kasar Somalia, da kuma Kenya, wadanda aka tusa keyarsu har filin
jirgi. Har wa yau dai sabon Shugaban ya hana a bada takardar shiga Kasar Amurka
ga mutanen Kasar Yemen, Iraki, Iran, Somaliya, Sudan, da kuma Kasar Siriya.
Har wa yau kuma Kasar Amurka na shirin aika Dalibai
zuwa Duniyar wata domin su girka giya kamar dai yadda muka samu labarai daga
Birnin Los Angeles na Kasar Amurka. Wannan ne dai karo na farko a tarihi da
Amurka tayi irin wannan abu.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment