– Ashe Kasar Amurka tana da labarin za a kifar da
Gwamnatin Buhari a 1985
– Babangida IBB
ya kifar da Gwamnatin Buhari a wani juyin mulki
– Ashe CIA ta Amurka ta san duk abin da zai faru
Wasu bayanan sirri da muke
samu daga Hukumar bincike ta Amurka watau CIA sun nuna cewa ashe Kasar Amurka
tana da masaniyar cewa za a hambarar da Gwamnatin Janar Buhari shekaru 30 da
suka wuce.
CIA tana da labarin wanda
zai kifar da Gwamnatin Janar Buhari da kuma lokacin da za a yi wannan juyin
mulki. CIA ta gano cewa za a yi wa Buhari juyin mulki a shekarar 1985 lokacin
da tattalin arzikin Kasar da kuma goyon bayan wasu ya fara tabarbarewa.
An dai samu rashin jituwa a
tsakanin Sojojin Kasar musamman kanana da suka fito daga Kudancin Kasar lokacin
Janar Buhari yana mulkin Soji. Tun lokacin dai CIA tace ba za a dade ba, za a
kifar da Gwamnatin sa.
A jiya kuma Fadar Shugaban Kasa
ta bayyana cewa hutu ya kai Shugaba Buhari Landan ba ganin Likita ba. Femi
Adesina; Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai yace yanzu haka
Shugaba Buhari ba ya wani Asibiti.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment