Obasanjo yace ‘Yan Najeriya su komawa Allah
– Cif Obasanjo yayi wannan kira ne a Garin Ogun
– Ana
ta murnar shiga sabuwar shekarar Miladiyya
Tsohon Shugaban Kasa Cif
Olusegun Obasanjo yace dole ‘Yan Kasa su komawa Ubangiji idan har suna so
abubuwa suyi kyau a shekarar nan da aka shiga. Tsohon Shugaban Kasar yayi
wannan kira ne a Garin su.
Jaridar Vanguard ta rahoto
cewa Tsohon Shugaban Kasan yayi wannan kira ga ‘Yan Najeriyar ne bayan an gama
Ibada a wani Coci da ke Garin Abeokuta na Jihar Ogun domin murnar shiga sabuwar
shekarar 2017.
Cif Olusegun Obasanjo dai ya
bayyana cewa a komai za a yi sai an saka Allah; siyasa ne ko harkar tattalin
arziki ne ko ma zamantakewa na rayuwa ne dole a tuna Ubangiji. Tsohon Shugaban
Kasar dai yace yana sa rai abubuwa za su yi kyau.
Kwanakin baya ne
Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Cif John Odigie-Oyegun yace Ubangiji ne ya
aikowa Kasar Najeriya Shugaba Buhari domin gyara ta. Shugaban Jam’iyyar APC
yayi wannan jawabi ne a wani lokaci a Garin Sokoto wajen taron ‘Ya ‘yan
Jam’iyyar na Jihar Kano.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment