–
Sabon Shugaban Kasar Amurka ya bada umarnin hana wasu baki shigowa Kasar Amurka
– Sai dai kuma Kotu ta dakatar da wannan shiri na Shugaban Kasar
– Wasu Kasashen sun fara maida martani
Kwanan nan, sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump
ya saka hannu kan wata doka da ta hana baki shiga cikin Kasar Amurkar. Hakan
dai ya sa aka tsare mutane kusan 200 da suke kokarin shigowa a filin jirgi.
Wata Kotu da ke Brooklyn ce dai ta cece Jama’a, inda
wani Alkali ya hana dabbaga wannan doka ta sabon shugaban Kasa Donald Trump.
Wannan doka dai ta Donald Trump ta shafi har wadanda suke dauke da katin zama ‘Yan
Kasar Amurka.
Ana ta zanga-zanga a Amurka, wasu ma na shirin neman rabewa daga Kasar
A Ranar Juma’a Donald Trump dai ya nemi a hana bakin
da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar na watanni hudu yayin da ya kuma
haramtawa ‘Yan Kasar Siriya shigowa Amurkar har abada. Kasar Iran dai wannan abu bai yi mata dadi ba, kuma ta fara shirin hana Amurkawa shigan Kasar.
A wani harsashe da NAIJ.com tayi, an fahimci cewa ‘Yan
Najeriya masu takardar shaidar zama ‘yan wata Kasar na iya fuskantar kalubale
musamman idan dayar Kasar ta su tana cikin guda 7 da Trump ya hana shiga
Amurka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment