Hudubar
Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria
RAUNIN MUSULMAI A YAU
Daga
Bakin Malam Farfesa Ibrahim Ahmed Aliyu
A’udh BilLahi
minas-Shaidanir Rajim…BismilalLahi Rahmanir Rahim
Dukkan yabo sun
tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu zuwa addinin Musulunci. Muna shaidawa
babu abin bauta da gaskiya sai Allah; wanda ya bamu addinin da ya fi kowane
addini watau Musulunci. Muna tabbatawa Annabi Muhammadu SAW bawa ne kuma Manzo
wanda ya cika alkawari. Duk wanda ya bi addinin Musulunci, tabbas ya samu gyadar
dogo. Allah ya dada tsira ga Annabin Sa, ya sa mu kuma mu tabbata cikin
Musulunci.
Bayan haka:
‘Yanuwa
Musulmai, da can a baya, Mu ne a gaban ayari, Mu ne ke rike da linzami na
ragamar al’ummar Duniya na wani lokaci. Mun yi jagoranci cigaban da babu irin
sa a da. A wancan lokacin, Musulmai sun hada ilmin Duniya da na lahira watau
hasken wahayi da na hankali. Cigaban Musulunci ya zama cigaba da babu irin sa,
harshen musulunci shi ne ya zama harshen cigaba. Jami’o’in Musulunci su ne wuri
na karatu ga dukkanin mutane daga ko ina a Duniya. Litattafan Muslunci sune
madogara a Duniya. Sunayen Malaman Musulunci ke haskaka ko ina a Duniya. Kai
karfin Musulmi ya kai lokacin da Khalifa Umaru Dan AbdulAziz ya ji labarin cewa
an kama wani Musulmi a matsayin Fursunan Yaki, Khalifa Umar AbdulAziz ya
rubutawa Sarkin Rumawa takarda cewa: ‘Bayan gaisuwa, naji labarin ka kama wani
Musulmi, wanda Allah ya rubutawa martaba, sai kai ka wulakanta sa. Ina maka
kashedi cewa idan har wasika ta, ta zo maka, to ka sake sa. Idan ba haka ba,
zan zo maka da runduna wanda karshen ta inda kake, farkon ta kuma inda nake…’
Girma da daukakan Musulmi ya kai wani Khalifa na Daular Abassiya ya taba fadawa
wani girgije na damina a sararin samaniya: ‘Ya kai girgije, ko kayi gabas, ko
kayi yamma, ka yi ruwa inda duk ka ga dama, harajin ka sai ya zo ga Baitul-Mali
na Musulmai…’ Ma’ana ko yayi ruwa Kasar Musulmai, a samu Zakkah, ko kuwa inda
ba su ba, a samu haraji na jizya daga hannun wadanda ba Musulmai ba. A da can
Musulmai ke rike da Duniya, lokacin da muke rike da Musulunci. A lokacin akwai
jin dadi da kwanciyar hankali, sai dai lokacin da aka rabu da Musulunci sai
muka zama kaskantattu.
Ya ‘yan uwa yanzu
muna nan a danne mu, ana tursasa mu, mun zama koma-baya, ana yi mana cin kashi.
Ko me ya jawo haka? Shin ba mu da yawa ne? A’a! Wallahi muna da yawa! Yawan
Musulmai yanzu ya kusa Biliyan 2, sai dai yawan namu bai da amfani tamkar yawan
tsintsiya ba shara; kamar dai yadda Manzo SAW ya fada za mu zama kamar sharan
bisa ruwa, a wannan lokaci Al’ummomi za su rika wasoso a kan mu, kamar yadda
mayunwata suke wasoso a kan akushi. Dama Manzon Allah SAW yace za a cire
kwarjinin Musulmai a fuskar Mutane, sannan kuma za a same mu da rauni. Ko
menene wannan rauni da Manzon Allah SAW ya fada? Wannan rauni shine son
duniya da tsoron mutuwa. Sai ka ga mai rauni a da baya yayi galaba a
kan musulmi. Masu tsoron mutuwa sun afka mana, har kaskantattu sun koma suna
mana cin kashi. To gaskiya lalacewar zukatan mu ne ya jawo duk wadannan abubuwa
suka faru, ba shakka mun yi rauni kamar yadda Annabi SAW ya fada.
‘Yan uwa Musulmi
a gaskiya mun bar Musulunci, Allah SWT kuma ya bar mu. Ubangiji ya bar mu da
kawun mu, kuma duk wanda Allah SWT ya bari da kan sa, ba zai taba samun nasara
ba a nan Duniya da Lahira. Mafita kuma itace a komawa Musulunci, dole mu komawa
Addinin Musulunci gaba dayan mu. Musulunci kuma ba shi bane kafa dokoki watau
haddi na zina ko bulalan shan giya. Bari ma wannan wani bangare ne kadan daga
cikin bangarorin Musulunci; Surorin da suka saukar da Hukuncin laifuffuka sune
karshe daga cikin abin da aka saukar a Al-kur’ani. Ayoyin da suka yi magana
game da laifuffuka kididdigaggu ne idan aka kamanta da sauron Ayoyi, ba dai
wadannan bane kadai Addinin Musulunci. Saboda haka dole ne mu koma yi wa Jama’a
kyakkyawar tarbiya, tarbiya da za ta hana mutane bata daga hanyar Allah. Mutane
da dama dai sun fi damuwa da kafa dokokin Musulunci, wanda ko ba ya gina al’umma
ko raya zukata. Abin da ke gina Mutane shi ne tarbiya. Tun daga Gidajen mu da
kuma Makarantu da hanyoyin sadarwa za a yi wannan aiki na tarbiya. Da irin
wannan tarbiya ne mutum zai zama Musulmi na gari a ko yaushe yana tsoron Allah
ba tare da wani Dan Sanda ba. Mutum ya zama kamar wannan Budurwar nan ta zamanin
Sayyidina Umaru RA da ta ki kara ruwa cikin nono yayin da uwar ta ke nema tayi
algush, Budurwa tace da Uwa ta: Ai Umar RA
ya hana, sai Uwar tace: ‘Ai Umar RA bay a ganin mu..’ Budurwa kuwa tace:
‘ai Ubangijin Umaru yana ganin mu... Ko kamar Makiyayin nan da yace da Umaru RA
‘Ina Allah SWT yake?’ yayin da ya nemi jarraba Bawan nan da ya cuci Ubangidan
sa. Saboda haka Umaru RA ya ‘yan ta wannan Bawa yace idan ya ci gaba a haka, za
a ‘yan ta sa a Gobe Kiyama.
Ya ‘yan uwa
lokaci yayi da za mu gane mu su waye. Mu fa Musulmai ne, kuma dole mu rike
Musulunci. Idan har mu ka rike Musulunci; muna tare da komai, idan kuma mu ka
bar Musulunci; ba mu da komai. Babu kuma wanda ya isa ya hana mu wannan Addini.
Abin da muke so shine mu rayu, kuma mu mutu a Musulunci, muna masu takama da
wannan Addini. Allah SWT dai yace babu wanda ya fi kyakkyawar magana kamar
wanda yayi aiki na kwarai yayi kira ga Allah, ya kuma ce ina cikin Musulmai.
Allah ka daukaka
mu, ka wulakantar da abokan gaban mu. Allah muna hada ka da abokan gaban mu.
Allah ka sa mana kin kafirci da fasikanci da sabon ka. Allah ka sanya mu cikin
rahamar ka.
Ameen.
Muhammad
Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment