Thursday, January 19, 2017

Ka-ka-kara-ka-ka: An kai karar Shugaba Buhari


– ‘Yan Shi’a sun maka Shugaba Buhari kara a Majalisar dinkin Duniya


– Yanzu haka ana zanga-zangar ‘A saki Zakzaky’


Kwanan nan dai Shugaba Buhari zai yi tafiya na kwanaki 10




Kungiyar IMN ta ‘Yan Shi’a a Kasar nan ta kai karar Shugaba Buhari zuwa ga Majalisar dinkin Duniya da sauran Kasashen waje. ‘Yan Shi’a dai sun koka da yadda ake rike da Shugaban Kungiyar ta IMN, Ibrahim Zakzaky wanda yake daure a hannun Hukuma har yanzu.

Gwamnati dai tana cigaba da rike Ibrahim Zakzaky da matar sa, fiye da shekaru guda kenan. ‘Yan Kungiyar ta Shi’a suna neman a hukunta Kasar Najeriya saboda sabawa umarnin Kotu da tayi game da shari'ar Zakzaky.

Shugaban Kungiyar Shuhudah ta ‘Yan Shi’a, Sheikh AbdulHamid Bello yace bai dace Gwamnati ta cigaba da rike Shugaban Kungiyar na IMN ba, bayan babban kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a sake sa tuni. 

Shi dai Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwanaki 10. Shugaban Majalisar Dattawar Kasar, Bukola Saraki ya karanto takardar Shugaban Kasar, Osinbajo zai rike ragamar mulkin Kasar na wannan lokaci. 

'Yan Shi'a kuwa dai sai zanga-zanga suke yi a Kaduna da sauran birane na Najeriya; A Saki Zakzaky.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...