– Wani Mutumin Jihar Kano ya kashe wani
Direba da mari don yace Buhari ya rasu
– Har yanzu dai wannan Direba
bai san inda yake ba
– Ana ta yada rade-radin cewa
Shugaba Buhari ya rasu a Asibiti
Kamar
yadda Jaridar Vanguard ta fada, wani mutumi mai suna Usman Bukar ya yankawa
wani Direban mota mari har sai da ya kusa mutuwa don kuwa yace Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari ya mutu.
Wannan
abu dai ya faru ne a Jihar Delta tsakanin Direban motar haya da wani matashi
mutumin Kano. Wanda abin ya faru a gaban say ace mutumin ya yankawa Direban
mari ne bayan ya ji yana yada labarin cewa Shugaba Buhari ya rasu a wurin ‘yan
jarida.
Wannan
mutumi dai yace za a jefa gawar Shugaba Buhari a Kogin Neja domin halittun ruwa
su ci, ya kara da cewa Shugaba Buhari mugun mutum ne, nan ne fa Malam Usman ya
harzuka, ya ketawa wannan mutumi wani mugun mari, yanzu haka yana can wani
asibiti mai suna Temple Clinic da ke
Garin Asaba.
‘Yan
uwan wannan mutumi dai sun nemi rama abin da ya faru, sai dai Jami’an ‘Yan
Sanda sun shiga tsakani. Andrew Aniamaka, mai magana da bakin Hukumar ‘Yan
Sanda ya tabbatar da faruwar wannan abu. Yanzu haka Usman na hannu Jami’an
tsaro shi kuma wannan Direba na can Asibiti bai san halin da yake ciki ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment