‘Yan Sanda sun kama wani don yace
Shugaba Mugabe zai mutu
– Jami’an ‘Yan Sanda sun damke wani Fasto bayan ya bayyana ranar da shugaban kasa zai rasu
– Faston yace Mugabe zai rasu a
watan Oktoban shekarar nan
– A Kasar Zimbabwe dai bai halatta
kace shugaban kasa zai mutu ba
An
ce a bakin wawa ake jin mutuwar sarki. Ga wani Fasto ya gano ranar da shugaban
kasa zai mutu. Ko da ya bayyana kuwa, sai ‘Yan Sanda kuma kama sa da laifi.
Yanzu haka Patrick Mugadaza na hannun Jami’ai.
Wani
Faston Cocin Kariba mai suna Patrick Mugadaza ya bayyana cewa shugaban kasar
Zimbabwe, Robert Mugabe zai rasu a cikin watan Oktoban wannan shekarar, ko da
ya sanar da hakan sai ‘Yan Sanda suka kama shi. Shugaba Mugabe dai yana da
shekara 93 a Duniya ya kuma dade kwarai kan mulki.
A
wancan makon ne Faston yace an nuna masa cewa Mugabe zai rasu a Ranar 17 ga
watan Oktoban bana. A Kasar ta Zimbabwe bai halatta kace shugaban kasa zai mutu
ba. Don haka tuni ya shiga hannun Hukuma.
A
nan gida kuwa, kwanakin baya wani Fasto a Najeriya ya buga-ya gano cewa Shugaba
Buhari ba zai karasa mulkin Kasar nan ba. Malamin Addinin Kiristan ya bayyana
cewa ya leko cewa Shugaba Buhari zai rasu ne a cikin shekarar 2019 inda rashin
lafiya za ta ci sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment