Tuesday, January 17, 2017

An sace wani Likita a Sokoto



Wani Malamin Asibiti ya fada hannun miyagu masu garkuwa da mutane a Sokoto


Kungiyar Malaman Asibiti na Jihar Sokoto ta bayyana haka


Satar Jama’a dai ya zama ruwan dare a Kasar nan




Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an sace wani Malamin Asibiti a Garin Sokoto. Shugaban Kungiyar Malaman asibiti na Jihar, Abdullahi Aliyu ya bada wannan sanarwa ba da dadewa ba. Sunan wannan Jami’in Asibiti dai Bello Arzika.

Abdullahi Aliyu yace an sace daya daga cikin ‘ya ‘yan Kungiyar na sun a Malaman asibitin Najeriya watau MHUN. An sace Malamin lafiyar ne a Yau Litini kamar yadda Aliyu ya bayyanawa manema labarai. An dai yi gaba da Malamin ne bayan ‘Yan fashi sun tare su.

An sace Bello Arzika ne a hanyar Sokoto zuwa Isa kamar yadda NAN mai dillacin labarai ta bayyana. Yanzu dai an shiga Dajin Gundumi da Malamin kiwon lafiyar. Jami’an tsaro dai sun ce ba su da masaniya game da lamarin.

Arzika ya taba rike wani matsayi a Kungiyar ta 
Malaman asibitin Najeriya watau MHUN na shiyar Sokoto. 

Sata da garkuwa da Jama’a dai ya zama ruwan dare a Kasar, haka kwanaki a ka kama wani Tsohon Malamin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a hanyar sa ta Abuja.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...