Thursday, January 19, 2017

Man Utd ta fi kowa kudi a Duniya


Yanzu Kungiyar Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya


Man Utd ta buge Kungiyar Real Madrid da Barcelona


Leicester City sun samu shiga sahun kungiyiyi masu kudi




Kungiyar kwallon kafan Man Utd ta Ingila ta kerewa kowace Kungiya kudi yanzu haka a Duniya. Man Utd ta doke Real Madrid wanda ke kan gaba a da shekara da shekaru. Real Madrid dai ta dawo na uku a jerin masu kudin Duniya.

Kungiyar Man Utd na da kudi har Dalar Euro Miliyan €689, sai kuma Kungiyar Barcelona ke biya da Miliyan €620.2 yayin da Real Madrid ke da Miliyan €620.1 a yanzu. Kungiyar nan ta Bayern Munich da ke Jamus ce ta hudu, sannan kuma Man City tana ta biyar.

Duk Duniya dai yanzu babu Kungiyar da ke jawo kudi irin Manchester United. Kungiyar Madrid dai ta fi shekara goma tana zuwa ta daya, sai dai bara Man Utd ta buge ta. Sauran Kulobs da suke cikin jerin sun hada da: Leicester, Inter Milan, West Ham, Schalke, AS Roma, Tottenham, Dortmund, At. Madrid, Arsenal, Liverpool, Juventus, dsr.

Kungiyyoin kwallon kafa na Ingila dai sun taka rawar gani bana. Wannan ne dai karo na farko da Man Utd ta zo ta daya tun shekarar 2003.
.

[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...