– Sai ga Amarya ta zo auren ta a cikin tarakta
–
Kawai sai aka hango Amarsi cikin motar gona
– Shi
kuma Ango ya hawo gingimari
An ga abin mamaki a kwanan
nan, yayin da wata Amarya ta hawo motar gona watau tarakta ta hallara wurin
daurin auren ta. An dai saba ganin Amare a kan dawaki ko keken su, amma da wuya
idan an taba samun wanda ta zo auren ta bisa tarakta.
Amarya Aisling Graham tace
bayan ta sa rigar ta, sai kawai ta kama tarakta ta hayo, ga kuwa taraktan nan
an yi mata kwalliya kamar yadda aka saba kawata abin hawan amare. Nan fa Amarya
Aislimg ta dunfaro wurin daurin auren na ta a cikin motar gona.
Aisling Graham tace tana da
sha’awar tarakta, tace tun tana yarinya karama ta ke tuka tarakta, don kuwa ta
taso ne cikin gidan noma. Tun Aisling tana karama dai tace a bisa tarkata ta
gona za ta hallarci auren ta. Mijin ma dai ba a bar sa a baya ba, don kuwa a
cikin wata gingimari aka hango gogan.
Kwanaki dai haka wani
Balarabe ya saki ‘Yar Amaryar matar sa jim kadan da daura masu aure. Ango ya ga
matar ba tare da kwalliyan da ya saba ba a karo na farko. Abdul Azeez Azif Asaf
mai shekara 34 ya rabu da amaryar sa ‘Yar shekara 28 yace ashe duk yaudarar sa
aka yi tayi a da da kayan shafa.
No comments:
Post a Comment