– Sojojin
Najeriya sun kara ceto wata daga cikin ‘Yan Matan nan da aka sace a Chibok
– Jaridar Sahara Reporters tace an tsinci yarinyar da
goyo
– Kusan
kwanaki 1000 kenan da sace ‘Yan Matan daga Makarantar su
A yayin da ake bakin cikin
cikar kwanaki 1000 da Boko Haram suka sace Yan Matan nan na Chibok daga
Makarantar su, Sojojin Najeriya sun ga guda 1 daga cikin su a wajen Dajen
Sambisa.
Labarai daga Sahara
Reporters na nuna cewa an samu Yarinyar ne tare da goyon wani da ake tunani na
ta ne. Sunan wannan Yarinya dai da Sojojin Bataliya ta 27 suka kubutar Rakiya
Abubakar.
An sami wannan Yarinya ne a
Ajigin da ke Karamar Hukumar Damboa. Wannan dai itace kusan ta 29 da ta baro
hannun Boko Haram tun bayana da aka sace su shekaru fiye da biyu da suka wuce.
An dai sace ‘Yan mata fiye da 200 a wancan lokaci.
Kwanaki dai an ceci wasu
daga cikin ‘Yan matan har wani Gwamna yake cewa kawai ana kokarin kauda
hankalin ‘Yan Najeriya ne daga halin da ake ciki a fadin Kasar na yunwa da
talauci.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment