– Kwastam
tayi wasu ‘yan sauyi a Gidan na ta
– Shugaban Kwastam din na kokarin shiryawa sabuwar
shekara
– Motoci kuma dai na nan a Kasa ba
a shiga da su ba
Shugaban Kwastam na Kasa,
Kanal Hammed Ali mai ritaya ya amince da wasu ‘yan sauye-sauye da aka yi a
Gidan domin shiryawa sabuwar shekarar nan da kyau. Sauyin da aka yi dai za su
taimaka wajen karawa Hukumar karfi kamar yadda aka fada.
An dai canzawa Manyan
Ma’aikata da dama wajen aiki, wannan mataki kuma zai fara aiki ne ba tare da
wani bata lokaci ba. Gidan Talabijin na Kasa watau NTA ta kawo wannan labara. A
cikin wadanda abin ya shafa akwai wasu manya har guda 46.
Cikin Wadanda abin ya shafa
akwai mataimakan Shugaban Kwastam din watau masu matsayin ACG har guda 8. Sun
hada da: Abdulkadir Azerema, Umar Sanusi, Mondau Abueh, Augustine Chidi,
Charles Edike, Aminu Dangaladima. Ahmed Muhammad, da kuma Francis Dosunmo.
Hukumar kuma ta kara
tabbatar da haramcin shigo da motoci ta Kasa. Yanzu haka dai akwai motoci makil
da ba a gama aikin karaso da su cikin gari ba a bakin iyakokin Kasar. Kungiyar masu shigo da motocin dai suna neman alfarmar watanni uku.
A bayan
nan ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin
Kasar nan ta iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da
tsofaffin motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment