Monday, January 16, 2017

TOFA: Dan Majalisa ya mutu a hannun ‘Yan Sanda


– Wani Tsohon Dan Majalisa ya mace a hannun Jami’an ‘Yan Sanda a Legas


– An dai tsare Honarabul Nze Duru ne a Ranar Alhamis, ya kuma cika Ranar Juma’a


– Sufeta Janar na ‘Yan Sanda ne dai ya sa aka kama sa




Wani Tsohon Dan Majalisar Kasar nan Honarabul Nze Duru ya cika a hannun ‘Yan Sanda a Ranar Jumua’ar da ta wuce. Jami’an ‘Yan Sanda sun kama Nze Duru a Legas a Ranar Alhamis, ya kuma ce ga Garin ku nan a Ranar Jumu’a.

Rahotanni na nuna cewa Sufeta na ‘Yan Sanda; Ibrahim K Idris ne ya bada umarnin kamo Tsohon Dan Majalisar. Honarabul Nze dai ya rasu ne a cikin dakin da yake tsare da ke Onikan a Jihar Legas. Ana zargin Honarabul din da yin gaba da wasu kudin fansho, sai dai a lokacin ya karyata zargin ya kuma zargi Jami’an ‘Yan Sanda da nuna rashin gaskiya a lamarin binciken.

A Gidan tsarin ne dai Honarabul din ya yanke jiki ya fadi. Honarabul Nze Duru ya bayyana cewa Mataimakin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda na Yankin Legas, Aderanti Kayode ya hana sa ganin Likita har sai da abubuwa suka tabarbare.


[NAIJ Hausa]



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...