Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai
albarka
- A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala
- Musulmai sun dauki wannan rana da muhimmanci
- Ranar Juma'a na daya daga cikin Ranakun Idin Musulunci
A
yau kuma mun koma zauren Addinin Musulunci ne inda mu ka tabo kadan daga cikin
falalar wannan rana ta Juma'a. Akwai sunnoni da dama da ake so a aikata a
wannan rana.
- Karbar
addua
Ya
zo a hadisin Bukhari da Muslim cewa akwai wani lokaci a wannan Rana da ba a
maida addua da zarar mutum yayi ta. Wannan na daga cikin falalar wannan Rana.
- Rubuta
lada
Duk
wanda ya isa masallaci kafin Liman ya iso ya gabatar da huduba yana da matukar
lada wanda Mala'iku ne za su sa shi cikin wani littafi. Iya saurin mutum iya
ladar da zai samu Inji Manzon Allah SAW.
- Kariya
daga Dujjal
Duk
wanda ya karanta Suratul Kahf zai samu tsari daga fitinannen da zai zo a
karshen zamani watau Dujjal. Haka kuma zai samu falala mai yawa har zuwa Juma’ar
wata makon.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment