–
A jiya ne aka samu wani kuskure daga Sojin Najeriya
–
Rundunar Sojin saman Kasar sun saki wani bam a sansanin ‘Yan gudun Hijira ba da
sani ba
– Mutane
kusan 2 ne kuma suka rasa rayukan su
A jiya ne dai aka samu wani matsala daga Sojojin
Najeriya; Sojin saman Kasar sun yi wani subul-da-bam a sansanin ‘Yan gudun
Hijira da ke Garin Rann. Wannan yayi sanadiyar mutuwar mutane 2, da dama kuma
sun raunana.
Shugaban Kasa yayi maza-maza ya mika ta’aziyar sa ga
wadanda abin ya shafa tare da yi masu addu’a. Femi Adesina ne yayi wannan
jawabi bayan faruwar abin. Shugaba Buhari ya mika ta’aziyar sa ga daukacin
al’ummar Jihar Borno.
Rundunar Sojin Kasar dai ta tabbatar da wannan kuskure
da aka samu wajen aiki ta bakin Birgediya-Janar Rabe. Gwamnatin Tarayya dai tayi alkwarin agazawa wadanda abin ya
shafa.
Haka kuma shekaran jiya aka kai wani hari na kunar bakin wake a Masallacin
Jami’ar UNIMAID ta Maiduguri da Asuba. An dai yi rashin sa’a mutane 5 sun rasu, ciki har da
wani babban Farfesa na likitan dabbobi mai suna Aliyu Usman Mani.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment